✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fitar da jadawalin gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Nahiyar Turai (Champions League)

A ranar Litinin da ta gabata ne Hukumar shirya gasar cin kofin zakarun kulob-kulob a Nahiyar Turai watau UEFA ta fitar da jadawalin gasar a…

Sepp Blatter, Shugaban Hukumar FIFAA ranar Litinin da ta gabata ne Hukumar shirya gasar cin kofin zakarun kulob-kulob a Nahiyar Turai watau UEFA ta fitar da jadawalin gasar a zagaye na biyu.
Ana sa ran kasashe 16 ne za su fafata a wasannin zagaye na biyun.
Za a yi wasan farko ne a ranakun Talata 18 da Laraba 19 ga Fabrairun 2014 yayin da za a yi wasa zagaye na biyu a ranakun Talata 25 da kuma Laraba 26 ga Fabairun 2014. Daga nan za a zubar da kasashe takwas sannan wadanda suka haye kuma za a sake hada su don buga wasa a matakin Kwata-Fainal.
Ana sa ran za a yi wasan kwata-fainal ne a ranakun Talata 11 da Laraba 12 da kuma Talata 18 da Laraba 19 ga watan Maris, 2014 ne kafin a tantance kungiyoyin da za su haye matakin kusa da na karshe watau Semi-Fainal.
Ga yadda jadawalin ya kaya kamar haka:
Manchester City da FC Barcelona
Olympiacos da Manchester United
AC Milan da Atletico Madrid
Bayern Leberkusen da PSG
Galatassaray da Chelsea
Shalke 04 da Madrid
Zenith da Dortmund
Arsenal da Bayern Munich