✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara zafin da ba a taba yin irinsa ba a tarihin Landan

Ana hasashen yanayin zai iya haifar da asarar rayuka

A karon farko a tarihi, za a yi zafin da ba a taba yin irinsa ba a birnin Landan da ke kasar Birtaniya, inda yanayi zai kai kimanin mataki 40 a ma’aunin celcius a ranakun Litinin da Talata.

Tuni dai jiragen kasa suka dakatar da ayyukansu, yayin da hukumomin lafiya suka tanadi motocin daukar marasa lafiya saboda jiran ko-ta-kwana.

Yankunan kasashen Turai da dama dai a ’yan kwanakin nan na fama da matsanancin zafi, yayin da wutar daji ke ci gaba da yaduwa a kasashen Portugal da Spain da kuma Faransa.

Tuni dai gwamnatin Birtaniya ta ayyana dokar ta-baci a kan yanayin da shi ne mafi tsanani, fiye da na 38.7 din da aka taba samu a shekarar 2019.

Wani Ministan gwamnatin Birtaniya, Kit Malthouse, ya shaida wa BBC cewa, “Muna cikin matsanancin yanayi a wadannan kwanakin guda biyu.”

An kuma karkafa allunan gargadi kan tsananin zafin ga masu tafiya a kafa a tashar Victoria da ke birnin na Landan.

Gwamnati ta kuma ba mazauna birnin shawarar takaita zirga-zirga matukar ba ta zama dole ba.

Wani ma’aikacin hukumar sufurin jiragen kasa ta birnin, Jake Kelly, ya ce ana sa ran harkokin sufurin su dawo ka’in da na’in ranar Laraba, lokacin da ake sa ran yanayin zafin ya sauka, kodayake ya ce hakan ya danganta da irin barnar da aka ga yanayin ya yi.

Galibi dai mazauna kasar na iya jure tsananin sanyi, amma ba sa iya jure zafi komai kankantar shi, kuma hatta gine-ginensu ba a yi su yadda za su dace da yanayin na zafi ba.