Rahotanni da ke fitowa daga Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) sun nuna an fara yunkurin sallamar kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Sunday Oliseh.
Kafar watsa labaran wasanni a yanar gizo ta www.footballibe.ng ta kalato cewa kalaman batuncin da kocin ya yi da wani gidan rediyon FM a kan hukumar da kuma rashin tabuka abin kirki a gasar cin kofin matasa na Afirka CHAN da yanzu haka ke gudana a Ruwanda na daga cikin dalilan da suka sa hukumar ta fara yunkurin korar kocin daga mukaminsa.
Oliseh wanda ya taba yi wa kulob din Jubentus na Italiya kwallo, ya fara samun takun saka da NFF ne jim kadan bayan an fitar da Super Eagles daga gasar CHAN a makon jiya. Rahoton ya nuna kalaman da kocin ya yi sun bata wa hukumar rai don haka take kokarin raba gari da shi.
A tattaunawar da kocin ya yi da gidan rediyon FM, ya nuna yadda NFF ta yi wa ’yan kwallon Super Eagles rikon sakainar kashi a Ruwanda. Hasalima ya nuna a lokuta da dama sai da ya yi amfani da kudin aljihunsa wajen tafiyar da harkokin kungiyar saboda karancin kudi da kungiyar ta yi fama da shi, duk da koken da suka rubuta wa hukumar ta NFF.
An ruwaito tuni Hukumar ta fara tuntubar Koci Samson Siasia a matsayin wanda zai iya maye gurbin Oliseh. Haka kuma Emmanuel Amuneke ne ake sa ran zai zama mataimakin Siasia idan hakan ta kasance.
Haka kuma yadda ran magoya bayan kungiyar a ciki da wajen Najeriya ya baci tun bayan da aka fitar da Super Eagles daga gasar CHAN inda suka rika kiran a kori kocin, na daga cikin dalilan da za su iya sanya wa a kori kocin.
Sannan a shekaranjiya Laraba Hukumar NFF ta bayyana cewa daga yanzu ita ce ke da alhakin zabo ‘yan kwallon da za su yi wasa da Masar a gasar neman gurbin hayewa cin kofin Afirka da za a yi a tsakanin Super Eagles da kuma Masar a wata mai zuwa.
Hakan ya nuna Hukumar NFF ta fara dawowa daga rakiyar Sunday Oliseh na bar masa wuka da nama wajen tafiyar da harkokin kungiyar, musamman wajen zabo ‘yan kwallon da za su kare martabar Najeriya.
Tuni wasu kococi da suka hada da Ley Roy da Herbe Bernard suka nuna sha’awar horar da Super Eagles idan aka sallami Oliseh daga mukaminsa.
Idan za a tuna a makon jiya ne kasar Gini ta fitar da Najeriya a gasar cin kofin matasa na Afirka CHAN da ke gudana a Ruwanda a zagayen farko, al’amarin da ya bata wa magoya bayan kungiyar rai. Hakan ta sa wasu suka rika yin kiran ya dace a kori Oliseh.
An fara yunkurin korar Sunday Oliseh
Rahotanni da ke fitowa daga Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) sun nuna an fara yunkurin sallamar kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles…