An fara yi wa al’ummar Jamhuriyar Nijar mazauna Najeriya rajistar katin zabe a Kalaba, babban birnin Jihar Kuros Riba a ranar Litinin.
Ayawain na mutum biyu masu yin rajistar, karkashin jagorancin Adamou Amadou za su shafe mako biyu a jihar domin su yi aikin rajistar.
- Sojoji Sun Dakile Harin ISWAP A Mafa
- Hukumomin da ake neman rushewa sun samu N226bn a kasafin 2023
- NAJERIYA A YAU: Yajin Aikin ASUU: Nasara Ko Asara?
Adamou Amadou, jagoran tawagar ya shaida wa Aminiya cewa, “An turo mu ne daga Ofishin Jakdancin Jamhuriyar Nijar da ke Abuja zuwa Kuros Riba domin muyiwa ’yan asalin Jamhuriyar Nijar rajistar katin zabe.”
Ya ci gaba da cewa, “Za mu shafe mako biyu a nan muna yin rajistar kuma duk inda dan Nijar yake ya samu labarin za mu zo domin Aikin.”
Jami’in ba bayyana cewa idan suka kammala da Jihar Kuros Riba za su tafi garin na Uyo na Jihar Akwa Ibom domin suci gaba da yin aikin a can.
Shuhaban Kungiyar Kasar ’Yan Nijar mazauna Kuros Riba, Nasiru Ishaqa, ya bayyana matakin da gwamnatun kasarsu ta dauka na turo wakilai a yi musu rajista da cewa “Abin farin ciki ne, abin a yaba ne.
“Zan zan tabbata sauran ’yan Nijar mazauna manyan garurukan Ikom da Ogoja su ma an yi musu rajistar,” in ji shi.
Al’umar sun fara kwarara zuwa wurin da ake yin rajistar a Unguwar Hausawa da ke layin Bagobiri a garin Kalaba.