Hukumar Kula da Bankuna da Kamfanonin Inshora ta Kasa (NDIC) ta fara tantance masu ajiya a bankunan 42 da aka rufe domin biyan su kudadensu.
Daraktar Tantance Hakkoki ta NDIC, Nurat Ajigbewu ta ce a ranar Litinin aka fara tantance masu ajiya a bankunan da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kwace lasisi a ranar 12 ga watan Nuwamba.
- An cafke direban da ya kutsa kai Masallacin Ka’aba
- A karon farko cikin shekara 397 duniyoyin Jupiter da Saturn za su hadu
“NDIC mai alhakin rufe bankunan da aka kwace wa lasisi a hukumance ta fara tantance masu ajiya a bankunan da ke da inshora domin biyan su kudadensu.
“Domin kammala wannan aiki hukumar na kira ga daukacin masu ajiya a bukanan da aka rufe dsu ziyarci rassansu domin ganawa da jami’an NDIC da ke kasa domin a tantance hakkokinsu dagar ranar Litinin 21 zuwa Alhamis 24 ga Disamba, 2020,”
Sanarwar da Kakakin NDIC, Bashir A. Nuhu ya fitar ta bukaci masu ajiyar da abin ya shafa da su je da takardun shaidar ajiya a banki, da wata takardar shaida domin saukake tantacewar.
Sunayen kananan bankunan da CBN ta rufe din a fadin Najeriya su ne:
- Hedgeworth Micro Finance Bank
- Future Growth Micro Finance Bank
- Bagwai Micro Finance Bank
- Ere City Micro Finance Bank
- Cafon Micro Finance Bank
- Akcofed Micro Finance Bank
- Gufax Micro Finance Bank
- Partnership Micro Finance Bank
- ICB Micro Finance Bank
- Onima Micro Finance Bank
- Hometrust (Nations) Micro Finance Bank
- Ringim Micro Finance Bank
- Bigthana Micro Finance Bank
- Rogo Micro Finance Bank
- Makoda Micro Finance Bank
- Takai Micro Finance Bank
- Bebeji Micro Finance Bank
- Ajingi Micro Finance Bank
- Garko Micro Finance Bank
- Kangiwa Micro Finance Bank
- Augie Micro Finance Bank
- Mopa Micro Finance Bank
- Solid Base Micro Finance Bank
- Ultimate Benefit Micro Finance Bank
- Ovidi Micro Finance Bank
- Kirfi Micro Finance Bank
- Credit Express Micro Finance Bank
- King Solomon Micro Finance Bank
- Riggs Micro Finance Bank
- Billionaire Blue Bricks Micro Finance Bank
- Susu Micro Finance Bank
- Wealthstream Micro Finance Bank
- Aguda Titun Micro Finance Bank
- Sapphire Micro Finance Bank
- Metro Micro Finance Bank
- Mountain Top Micro Finance Bank
- Unyogba Micro Finance Bank
- Wapo Micro Finance Bank
- Ibogun Micro Finance Bank
- Korede Micro Finance Bank
- Ahetou Micro Finance Bank
- Fufore Micro Finance Bank