✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara shirin yi wa Keshi jana’iza

Gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar gwamnatocin wadansu jihohi da iyalan mamacin sun fara shirye-shiryen yi wa tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles…

 Marigayi Stephen KeshiGwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar gwamnatocin wadansu jihohi da iyalan mamacin sun fara shirye-shiryen yi wa tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Mista Stephen Keshi jana’iza.
Rahotannin da ke fitowa sun nuna gwamnatin tarayya za ta hada gwiwa ne da Jihohin Edo da Delta da kuma Kuros Ribas wajen yi wa mamacin jana’iza  inda ake sa ran za a binne shi ne a mahaifarsa da ke Illah ta Jihar Delta.
Kamar yadda rahoton ya nuna, za a fara shirin binne mamacin ne a Abuja inda ake sa ran John Mikel Obi zai jagoranci ’yan kwallon Super Eagles wajen yin ban kwana da gawar mamacin.
Haka kuma ana sa ran isowar ’ya’yan marigayin daga Amurka don su halarci bikin binne marigayin. Tuni dan uwan mamacin Sylbester Keshi ya sanar da cewa a ranar 28 ga watan Yuli ne za a yi bikin binne shi a Illah ta Jihar Delta.
Marigayin dai ya rasu ne a Jihar Edo a makon jiya bayan kwana uku kuma sai tsohon kocin kungiyar Amosu Shu’aibu shi ma ya rasu a Jihar Edo.