Shirin gina gidaje dubu 300 a kananan hukumomin kasar nan 774 da gwamnatin tarayya ta tsara yi don sayarwa ga masu karamin karfi, ya fara a yanar gizo, bayan kaddamar da dandalin a ranar Laraba, a birnin Abuja.
Da ya ke jawabi ga ‘yan jarida a yayin bikin, babban Darakta na kamfanin gine-gine na Family Homes Fund, da ke jagorantar aikin hadin gwaiwar, Mista Femi Adewole, ya ce dandalin mai adireshin (www.nshp.gov.ng), zai taimaka wajen samar da bayanai a kan hanyar da a ke bi wajen mallakar gida a shirin, wanda zai fara da gidaje dubu 2 a Unguwar Deidei Abuja.
- Daliban GSSS Kankara da aka sace suna raye — DHQ
- Kudin makamai: Kotu ta soke daurin da aka yi wa Olisa Metuh
- ‘Rubewar albasa ta haddasa tsadarta a Najeriya’
Ya ce farashin gidajen da za a gina ya fara ne daga naira miliyan 2, wanda kuma za a rika biyan naira dubu 9 a duk wata, sannan a kammala biya a cikin shekara 20, inji shi.
Daraktan wanda ya yabawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan kaddamar da shirin, ya ce zai taimaka wajen samar da ayyukan yi sama da miliyan 1 da dubu 800, ta hanyar aikin ginin, da kuma sayan kayan aiki daga kamfanonin gida da adadinsa zai kai kashi 90 a cikin dari.
Shugabar gidauniyar ’yan sanda ta samar da gidaje ga ma’aikatan rundunar, Femi Olomola-Sijuwade wadda ta bayyana farin ciki da lamarin, ta ce hukumarsu na cikin tsarin hadin gwiwa a shirin don ganin ’yan sanda masu karamin mukami sun mallaki gida na kansu a wuraren, wanda ya kunshi daidaikun jama’a da kamfanoni ko kungiyoyi da ke da sha’awar mallakar gida, don mambobinsu da su ka cancanta.
Shugaban kungiyar masu samar da rukunin gidaje na Najeriya Dokta Aliyu Wamako, ya bukaci gwamnatin da ta tabbatar da dorewar shirin, wanda ya bayyana a matsayin mataki na tallafawa tattalin arzikin kasa musamman a irin wannan lokaci da ake fama da karancin kudi a hannun mutane.
Sai dai ya ce adadin gidajen da za a gina a daukacin jihohin Najeriya da kuma Abuja, sun yi kadan idan a ka yi la’akari da gibin da a ke da shi na karancin mahalli a tsakanin jama’a, da ya ce ya kai na gidaje miliyan 22, a halin yanzu.