✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara rusau a kasuwar garin Lafiya

A ranar Litinin da ta gabata ne wasu taraktoci suka rushe shaguna da ke cikin Babban Kasuwar garin Lafiya da ke Jihar Nasarawa.  Da take…

A ranar Litinin da ta gabata ne wasu taraktoci suka rushe shaguna da ke cikin Babban Kasuwar garin Lafiya da ke Jihar Nasarawa. 

Da take zanta wa da manema labarai a lokacin rushe-rushen Babban Sakatare a Ma’aikatar Cinikayya da Ayyuka Misis Asibi Omary Agabu ta bayyana cewa gwamnatin jihar ta yi hakan ne da nufin rage cunkuso a kasuwar. Ta ce gwamnati ta riga ta samar wa ’yan kasuwan shaguna a kasuwar zamani da ta gina a Lafiya, inda ta shawarce wadanda ba su tare a sabuwar kasuwar ba, su yi hakan.
Shima anasa bangaren Babban Manaja a Ma’aikatar NUDB Alhaji Adamu Sule ya jinjina wa matakin gwamnati na canja wa ’yan kasuwar matsuguni, inda ya ce hakan ba shakka zai taimaka wajen tsara gine-ginen Lafiya yadda ya dace. Shugaban ’yan kasuwa a jihar Alhaji Shammasu dantsoho ya yaba wa gwamnati dangane da aikin, inda ya shawarci ’yan kasuwan su dauki lamarin a “matsayin ci gaba a gare su da sauran al’ummar jihar baki daya.”
Idan za a iya tunawa a makon jiya ’yan kasuwar suka gudanar da zanga-zangar adawa da yunkurin gwamnatin jihar na canja musu matsuguni daga kasuwar zuwa sabuwar kasuwar zamanin da ta gina.