✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara rububin ’yan kwallon Super Eagles a Afirka ta Kudu

Jim kadan da kammala gasar cin kofin Afirka ta ’yan gida CHAN a ranar Asabar ta makon jiya ce kungiyoyin kwallon kafa da dama a…

Jim kadan da kammala gasar cin kofin Afirka ta ’yan gida CHAN a ranar Asabar ta makon jiya ce kungiyoyin kwallon kafa da dama a Afirka ta Kudu suka fara rububin dauke wasu daga cikin ’yan kwallon Najeriya Super Eagles da suka fafata a gasar.
Najeriya ce ta zo na uku a gasar bayan ta doke Zimbabwe da ci daya mai ban haushi a wasan neman matsayi na uku.
Daga cikin kulob-kulob da ke zawarcin ’yan kwallon Super Eagles akwai Kaizer Chiefs da Orlando Pirates da Mamelodi Sundowns da Free Stars da kuma kungiyar kwallon kafa ta Supersport United.
Wasu daga cikin ’yan kwallon Najeriya da ake zawarcin sun hada da dan kwallon da ya fi nuna kwazo a gasar Ejeki Uzoenyi da masu tsaron baya Azubike Eguekwe da kuma Solomon Kwambe.
Rahoton da kafofin watsa labarai suka kalato ya nuna ’yan kwallon da ake zawarci ba su biyo takwarorinsu dawowa Najeriya bayan kammala gasar ba da hakan ya tabbatar da yunkurinsu na zama a Afirka ta Kudu don cigaba da yin wasan kwallo.
Rahoton ya kara da cewa tun bayan da Najeriya ta doke kungiyar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu a gasar ce kungiyoyin kwallon kafar suka fara rububin dauke ’yan wasan.
Kocin Super Eagles Stephen Keshi ya tabbatar da wannan labari a wata tattaunawa da ya yi da ’yan jaridu a Afirka ta Kudu jim kadan bayan an kammala gasar inda ya ce akwai yiwuwar ’yan kwallon su sanya hannu a Afirka ta Kudu don cigaba da yin kwallo.