Rahotannin da ke fitowa sun nuna kulob da dama ne a Ingila suka fara zawarcin tsohon dan kwallon FC Barcelona na Sifen Ronaldinho.
A wata tattaunawa da jaridar The Times ta yi da dan uwansa mai suna Roberto ya nuna yadda a kullum Ronaldinho yake samun kira daga kungiyoyin kwallon kafa daban-daban a Ingila da ke nuna sha’awar dauke dan kwallon.
Sai dai ya ce akwai yiwuwar dan kwallon ba zai koma Ingila don hankalinsa ya fi karkata ne zuwa Amurka ko yankin Asiya don cigaba da yin kwallo a can.
“dan uwana Ronaldinho a kowane lokaci yana so ya kasance a kungiyar da ke samun nasara ce. Har yanzu yana son ya cigaba da buga kwallo, hasalima bai taba samun mummunan rauni a tarihin kwallonsa ba, don haka ina ganin zai iya cigaba da yin kwallo nan da shekaru uku ko hudu masu zuwa”.
Shi dai Ronaldinho ya taba yi wa kulob din FC Barcelona na Sifen kwallo ne a tsakanin shekarar 2003 zuwa 2008. A shekarar 2008 ce ya koma kulob din AC Milan na Italiya daga nan ya bar kulob din a 2011.
Ya yi wa kulob din Fluminense na Brazil wasa sau biyu a lokaci daban-daban sannan ya yi wa kulob din Atletico Mineiro da na kueretaro duk a Brazil wasa.
Ronaldinho dai ya taba rike kambun Gwarzon dan kwallon duniya a lokacin da yake kwallo a kulob din FC Barcelona na Sifen.
An fara rububin Ronaldinho a Ingila
Rahotannin da ke fitowa sun nuna kulob da dama ne a Ingila suka fara zawarcin tsohon dan kwallon FC Barcelona na Sifen Ronaldinho.A wata tattaunawa…