✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara raba wa almajirai tabarma da gidan sauro a Yobe

Hukumar Ilimin Larabci da Musulunci ta Jihar Yobe (AISEB) ta fara rabon tabarmi da gidajen sauro ga almajirai a fadin jihar

Hukumar Ilimin Larabci da Musulunci ta Jihar Yobe (AISEB) ta fara rabon tabarmi da gidajen sauro ga almajirai a fadin jihar.

Sakataren Zartarwa na hukumar, Malam Umar Abubakar ya cen tabarmi da gidajen sauron tallafi na daga cikin kokarin da gwamnati ke yi na inganta walwala da rayuwar almajiran makarantun tsangaya a fadin jihar.

A cewarsa, shirin ya yi daidai da umarnin da gwamnatin jihar ta ba hukumar na tabbatar da kulawa da kuma tallafa wa yara almajirai.

Ya bayyana cewa an tsara rabon ga ɗalibai 100 a kowace karamar hukuma cikin kananan hukumomin Jihar 17, wanda za a fara daga makarantun Goni Yahaya da Goni Muhammad Tsangaya da ke Damaturu.

Ya ƙara da cewa, kayayyakin za su taimaka wa almajirai su kasance da cikin tsafta da walwala, kuma hukumar za ta ƙara kaimi wajan samar da abubuwa kamar su ciyarwa, sutura, da samar da kayayyakin koyo da koyarwa.

A nasa jawabin godiya, shugaban makarantar Goni Muhammad Tsangaya Malam Goni Muhammad ya bayyana tallafi a matsayin wanda ya dace, kuma zai iya canza rayuwar almajiran, yana mai kira ga ƙungiyoyi da ɗaifaikun mutane da su yi koyi da irin wannan matakin.

“Hakan zai taimaka matuƙa wajen inganta rayuwar ɗalibanmu, musamman wajen hana kamuwa da cututtuka da sauro ke haifarwa da kuma samar da kwanciyar hankali yayin barci,” in ji shi.

Ana sa ran ci gaba da rabon kayayyakin nan da makonni masu zuwa a dukkan kananan hukumomin jihar 17.