Rahotanni garin Gashuwa da ke Jihar Yobe sun ce an fara gyaran makabartar garin wacce ruwan sama ya lalata.
Hakan na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan wani rahoto da Aminiya ta fitar kan yadda ambaliyar ruwan sama ya lalata kaburbura da dama a makabartar.
- Gobara ta kashe mutum 64 a wurin killace masu COVID-19
- An kashe mutum 222, an yi wa 20 fyade a wata 3 a Kaduna – Rahoto
Rahotanni sun ce akalla kaburbura 650 ne suka burma sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a karshen mako.
Gwamna Jihar ta Yobe, Mai Mala Buni ne ya ba da umarnin gyaran makabartar bayan samun rahoton halin da ta ke ciki.
Buni ya bada umarnin fara gyaran ne karkshin Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA).
Shugaban Hukumar a Jihar, Dokta Mohammed Goje ya shaida wa Aminiya cewar tuni aka kai kayan aikin da za a yi amfani gyara makabartar.
Kazalika, wani magidanci mazaunin yankin mai suna Yahaya Mato, ya shaida shaida wa wakilinmu cewar tuni mota ta jibge bulo da siminti don fara aikin.
“Mun tare hanyoyin da ruwa ya balle jiya, muna godiya ga gwamnatin Jihar Yobe kan daukar matakin gaggawa,” a cewarsa.