Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya a ranar Litinin ta fitar da jadawalin jarrabawar daukar aiki ’yan sanda da kwararru a fannoni daban-daban a Jihar Kaduna.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ne ya bayyana cewa, “An shirya gudanar da jarrabawa da tantance lafiyar masu neman shiga aikin dan sanda daga ranar 16 zuwa 30 ga Afrilu, a Kwalejin ’yan sanda ta Kaduna.”
Ya ce duk masu neman aikin su taho da farar riga da guntun wando da taklami sau ciki.
- Soja ya caka wa dan acaba wuka a ciki
- Gwamnatin Katsina Ta Sayo Motoci Masu Sulke Don Yaƙar ‘Yan Bindiga
An kuma bayyana cewa, duk mai neman aiki ya taho da takardar gayyata da hukumar ta tura da katin shaidar dan kasa, da kuma shaidar gwajin lafiya daga wurin kwararren likita.
Rundunar ta bayyana cewa masu bukatar ƙarin bayani za su iya shiga shafinsu na intanet.
Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya ya bayyana cewa sanarwar ta ce, “Yana da mahimmanci a lura cewa waɗan da aka gayyata masu kwarewa ta musamman za su yi gwajin abin da suka kware aiki ne maimakon rubutacciyar jarrabawa”