✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara gasar rukunin Premier na biyu na Kano

A ranar Lahadin da ta gabata ce aka bude gasar rukuni na biyu wanda aka fi sani da Dibision II Premier League da Hukumar kwallon…

A ranar Lahadin da ta gabata ce aka bude gasar rukuni na biyu wanda aka fi sani da Dibision II Premier League da Hukumar kwallon kafa ta Jihar Kano ta dauki nauyin gudanar da shi.  

An gudanar da wasa na farko ne a filin wasa na Sani Abacha, inda kulob din Hotoro Classical ya buga wasa da kofar Ruwa Stars inda aka tashi canjaras.  

Alhaji Sharif Inuwa Ahlan shi ne Shugaban Hukumar Wasan kwallon kafa ta Jihar Kano ya bayyana wa manema labarai cewa kimanin  kungiyoyi 172 , da suka kunshi rukuni 26 ne za su buga wannan wasa a Jihar Kano.

Shariff Ahlan ya ce hukumar ta yi shiri sosai don magance rigingimu a tsakanin kungiyoyin  ta hanyar gudanar da taron kara wa juna sani da wayar da kai ga kungiyoyin. “Kafin fara wannan wasa mun gudanar da taron kara wa juna sani don kowace kungiya ta fahimci hakkinta da kuma hakkin ’yar uwarta da suke buga gasar, misali idan an samu canjin sheka ko kungiya, to wannan kungiyar ta tabbata ta biya ’yar uwarta kudaden da suka kamata ta biya don kada a samu  rigima a tsakaninsu. Na yi imani a wannan lokaci za a samu cikakken hadin kai wajen gudaarwa. Insha Allahu ba za a samu irin rigingimun da aka saba samu a baya ba,” inji shi.

Shugaban ya ce hukumarsu ta dauki duk matakin da ya kamata wajen yin gyara a harkar gasar, musamman game da yadda ake gudanar da alkalancin wasan. 

Sharif Ahlan ya kuma nanata cewa hukumarsa ta dauki wannan wasa da muhimamnci don haka za ta sa ido kan duk wani abu da zai bunkasa gasar tare da tabbatar da cewa ana gudanar da kowace  gasa yadda ya kamata.