✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara gasar Kofin Zaman Lafiya na Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna

A ranar Asabar da ta gabata ce aka fara gasar cin Kofin Zaman Lafiya na Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dokta Hadiza Sabuwa Balarabe a garin…

A ranar Asabar da ta gabata ce aka fara gasar cin Kofin Zaman Lafiya na Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dokta Hadiza Sabuwa Balarabe a garin Kafanchan da ke Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, inda ake sa ran kulob-kulob din kwallon kafa 40 daga kananan hukumomi takwas na Kudancin Kaduna za su fafata a kai.

Wasan wanda zai kasance da zaran an ci kulob wasa daya zai fita daga gasar, ana sa ran bayan kwana 20 za a kammala zagayen farko na wasa inda kungiyoyi 20 za su rage.

Yayin da yake jawabi wajen bude gasar, wakilin Mataimakiyar Gwamnan, Honorabul Buje, wanda har ila yau shi ne Mataimaki na Musamman ga Kwamishinan Matasa, ya yi kira ga jama’ar Kudancin Kaduna su yi amfani da wannan wasa wajen kara dankon zumunci a tsakanin kabilu daban-daban kuma mabiya addinai daban-daban daga garuruwa daban-daban da ke yankin da a baya ya yi kaurin suna wajen rikice-rikice.

Wanda ya shirya gasar, wani matashi mai kishin kwallon kafa, Ibrahim Ahmadu (Alake), ya ce ya shirya gasar ce don nuna wa duniya irin kwanciyar hankalin da aka samu a yankin, wanda hakan ya sa babu wata karamar hukuma da ke yankin da ba ta a cikin gasar.

“Matasan wannan yanki sun yardar su rungumi juna su zauna lafiya, wanda shirya wannan wasa ya samu ne sakamakon haka. Kuma mun yanke shawarar yin amfani da sunan Mataimakiyar Gwamnan Jihar ce kasancewarta ’yar asalin yankin wacce kuma take kaunar zaman lafiya inda hakan ya sa zuwa yanzu hatta wadanda ba su zabe ta ba suna yaba mata da yadda take rungumar kowa ba tare da la’akari da kabila ko addini ba,” inji shi.

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Jihar Kaduna Shareeff Abdullahi Kassim, wanda dan cikin garin Kafanchan ne ya yi kira ga dukkan kungiyoyin da ke taka leda a gasar su zamo masu biyayya ga dokokin wasa da shugabannin wasa tare da rungumar kaddara ga duk kungiyar da aka fitar don a kammala lafiya.

Zuwa yanzu kungiyar kwallon kafa ta Ginger United da ke cikin garin Kafanchan ta cire takwararta mai suna Young Stars da ke cikin garin Zangon Kataf da ci 3-1 yayin da Bridge Strikers da ke Gidan Waya ta doke takwararta ta Dangoma United da ci 2-0.

Sauran kungiyoyin da suke fafatawa sun hada da FC Poster daga Kachiya da Kwoi Selected da Jaba da Kagarko United da Jere United da Kubacha Selected da Jama’a Emirate da Kagoro Selected da Gwantu United da sauransu.