A makon jiya ne aka fara gasar wasan kallon kafa tsakanin kafofin watsa labarai da ke Jihar Kano.
Gasar wasan kwallon kafar mai taken “Kofin Gwamna Ganduje” kungiyar Marubuta Labarin Wasanni ta Jihar Kano (SWAN) ce ta shirya shi.
A rukuni na farko na gasar wanda aka yi a filin wasa na Sani Abacha, kungiyar Ma’aikatar Watsa Labarai ta jihar ta yi canjaras ne da takwararta ta Gidan Talabijin na NTA Kano da ci 1-1. Sai kungiyar ’yan wasan Gidan Rediyo Pyramid ta samu nasara a karawar da ta yi da takwararta ta Rediyo Kano da ci 2-1.
Haka kuma kungiyar Gidan Rediyon Edpress ta yi nasara a kan takwararta ta Correspondence Chapel da ci 3-1. Sai kuma fafatawar da aka yi tsakanin kungiyar Gidan Rediyon Freedom da NTA Kano inda aka tashi da 0-0 wato babu ci. Haka kuma kungiyar Gidan Rediyon Rahama ta yi nasara a kan takwararta ta gidan Talabijin na ARTb.
A zagaye na biyu na gasar kuma kungiyar Ma’aikatar Watsa labarai ta yi nasara ne a kan takwararta ta Gidan Rediyon Freedom. Haka kuma an tashi da 1-0 a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Gidan Rediyon Kano da takwararta ta Talabijin wato NTA. Amma a wasan da aka buga tsakanin gidan Rediyon Edpress da na gidan Rediyon Rahama, Edpress din ce ta yi nasara da ci daya mai ban haushi. An buga 1-1 a taskanain Correespondence Chapel da takwararta ta Raypower.
Idan muka koma fafatawar da aka yi tsakanin kungiyar Gidan Rediyon Pyramid da takwararta ta gidan Rediyon Freedom, Pyramid din ce ta samu nasara da ci daya mai ban haushi.
A jawabinsa Shugaban kungiyar Marubuta Labarin Wasanni na Jihar Kano Rilwanu Idris Malikawa Garu ya gode wa kafofin watsa labarai da ke Kano saboda hadin kan da suke bayarwa wajen samun nasarar gasar. Malikawa ya bayar da tabbacin kungiyar za ta ci gaba da yin kokari wajen shirya wasu tsare-tsare da za su kara ciyar da kungiyar gaba.
An fara gasar kafofin watsa labarai don lashe kofin Ganduje
A makon jiya ne aka fara gasar wasan kallon kafa tsakanin kafofin watsa labarai da ke Jihar Kano.Gasar wasan kwallon kafar mai taken “Kofin Gwamna…