An fara gasar cin kofin kwallon kafa na jami’in hulda da jama’a na kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta Nijeriya [NULGE] reshen jihar
Kaduna Kwamared Ahmed Tiyaye a ranar Larabar da ta gabata a babbanfilin wasa na garin Saminaka.
Da yake zantawa da wakilinmu kan wannan gasar kwallon kafa, shugaban shirya gasar, Yusuf Ibrahim Pate Lere ya yi bayanin cewa kungiyoyi
kwallon kafa 16 daga mazabu 11 na karamar hukumar Lere ne za su fafata a wannan gasar cin kofi.
Ya ce ganin irin baiwar da Allah ya yi wa matasan karamar hukumar kan harkokin wasan kwallon kafa, ya sanya aka sanya wannan kofi don a fito da irin wadannan matasa.
Ya ce muna son mu ga cewa ana daukar yaran wannan yanki a manyan kungiyoyin kafa na kasar nan.
Ya yi kira ga ‘yan siyasar yankin kan su rika tallafawa harkokin wasanni.
A ranar da aka fara gasar, kungiyoyin kwallon kafa na Greater Saminaka Academy da Shooting Stars Saminaka ne suka fara fafatawa. An tashi wasan Saminaka Academy ta samu nasara da ci daya mai ban haushi.
An fara gasar cin kofin Kwamared Ahmed Tiyaye
An fara gasar cin kofin kwallon kafa na jami’in hulda da jama’a na kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta Nijeriya [NULGE] reshen jiharKaduna Kwamared Ahmed Tiyaye…