✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara biyan malaman jami’ar da suka balle daga ASUU albashinsu na wata 8

Wani malami a jami'ar OAU ne ya tabbatar da hakan ga Aminiya

Gwamnatin Tarayya ta fara biyan malaman jami’o’in da suka balle daga kungiyar ASUU suka shiga sabuwar da aka kafa mai suna CONUA albashin da suke bi bashi na tsawon wata tawkas.

Malaman jami’o’in gwamnati a Najeriya dai sun shafe tsawon wata takwas suna yajin aiki, kuma tsawon wannan lokacin gwamnatin ba ta biya su albashi ba.

Daga bisani dai gwamnati ta kafa sabuwar kungiyar malaman jami’o’in ta CONUA don ta zama kishiya ga ASUU.

Wani malamin jami’a wanda mamban CONUA ne da kuma yake koyarwa a Jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife, wanda kuma ya nemi a sakaya sunansa ne ya tabbatar wa Aminiya hakan.

Ya ce tuni shugabancin kungiyar ya sami tabbacin alamun fara biyan kudin daga Ministan Kwadago, Chris Ngige.

Malamin ya ce Minista Ngige ya ba su tabbacin cewa za a fara biyansu kudadensu daga ranar Litinin, kuma hatta gibin da aka samu wajen biyansu rabin albashi a watan Oktoba za a gyara.

“Mu ba mu shiga wancan yajin aikin da aka yi na kwanakin baya ba. Mun rubuta wa Ministan Kwadago wasika, kuma ya ba da umarnin a duba batunmu don a fara biyan mu,” inji shi.

Sai dai duk kokarin wakilinmu na jin ta bakin Shugaban CONUA na kasa, Niyi Sunmonu, ya ci tura ya ci tura, saboda bai amsa kiran wayarsa ba.

Kazalika, bai amsa sakon kar-ta-kwanan da muka tura masa ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Da wakilin namu ya tuntubi mai magana da yawun Minista Ngige, Olajide Oshundun, ya tabbatar da cewar za a fara biyan mambobin na CONUA matukar ba su shiga yajin aikin na wata takwas ba.