Gwamnatin Tarayya ta fara bincikar ayyukan da Majalisar Zartarwa ta Kasa (FEC) ta bayar a aiwatar a shekarun 2017/2018 a sassan Najeriya, domin gano halin da ayyukan ke ciki.
Ministan Ayyuka na Musamman, George Akume ya kaddamar da binciken ganin inda ayyukan suka kwana da ido da nufin tabbatar da aiwatar da dukkannin ayyukan da FEC ta bayar kamar yadda aka tsara daidai da manufar gwamanti domin amfanin ’yan Najeriya.
- Ayyukan noma: Hukumar NDE na horas da mutum 100
- Abin da ya kamata ku sani kan shirin tallafin gwamnati na Survival Funds
Ma’aikatun da za a bibiyi ayyukan da aka ba su ne su ne: “Ma’aikatar Noma, Albarkatun Ruwa Ayyuwa da Gidaje, Lantarki, Sufurin Jiragen Sama, Birnin Taryya; sai kuma Hukumar Tasoshin Jiragen Ruwa da ta Kashe Gobara”, inji kakakin ma’aikatar, Julie Osagie ta bayyana.
Ta ce tawagar masu binciken ayyukan za su duba ayyuka a yankunan Arewa ta Tsakiya, Arewa ta Gabsa da Kudu maso Yamma daga ranar 21 zuwa 25 ga watan Satumba, bayan tawagar farko ta duba na sauran yankunan daga ranakun 14 zuwa 18 ga watan.
Jama’iar ta ce kafin fara aikin sai da ma’aikatar da hadin gwaiwar kwararru da Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsare da kuma Ofishin Bibiyar Ayyuka na Kasa suka horas da jami’an kan yadda aka tantace inganci da nagartar ayyuka a lokacin zagaye.
Sai dai Darektan Lura da Kudurorin Gwamnati na ma’aikatar, Davis Dashe, ya ce wasu zababbun ayyuka ne za a bibiya a ma’aikatu da hukumomin guda takwas.
Ya kara da cewa ma’aikatar ce kadai ke da hukumin bibiya da kuma sanya ido a kan matsayar da cimma a FEC domin tabbatar da an aiwatar da su yadda aya kamata.