Masu aikin ceto sun fara ɗebe ƙauna ga yiwuwar samun mutane da da ransu a ɓaraguzan girgizar ƙasar Morocco.
Mako guda ke nan da aukuwar girgizar kasar mai ƙarfin maki 6.8, wadda ta yi ajalin mutane kimanin 3,000, wasu akalla 5,000 suka jikkata.
- ‘Mutanen da suka mutu a ambaliyar Libya za su iya kai wa 20,000’
- Girgizar kasa 3 mafiya muni a Morocco
Girgizar kasar ita ce mafi muni cikin shekaru 60 a Morroco, inda a halin yanzu dubban mutane da suka tsallake rijiya da baya ke neman agaji a matsugunan jinƙai na wucin gadi a sassan ƙasar.
Tun bayan aukuwar girgizar ƙasar ranar Juma’a da dare ake aikin ceto a yankin Marrakech mai tsaunuka, inda kawo yanzu jami’an ceto suka ce sun daina jin ɗuriyar masu numfashi a cikin ɓaraguzai.
Duk da haka, ko a ranar Laraba sai da aka ceto wasu mutane da ransu a wasu yankuna masu tsauni da girgizar kasar ta shafa.
Wani jami’in agaji ya bayyana cewa yanayin hanyar shiga wurin ya zame musu kalubale, amma akan samu mutane da ransu.
A yayin da gwamnatin ƙasar ke ci gaba da jagorantar aikin ceto da kuma rabon kayan tallafi ga masu bukata, waɗanda suka jikkata na da matuƙar buƙatar magunguna.
Wadanda suke a matsugunan wucin gadi da gwamnatin ta samar kuma suna matukar bukatar abinci da tantuna.