✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fadakar da mata kan yadda za su gudanar da rayuwarsu

kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya (FOMWAN) reshen Jihar Yobe ta yi taron fadakar da mata hanyoyin da za su bi wajen gudanar da rayuwarsu kamar…

kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya (FOMWAN) reshen Jihar Yobe ta yi taron fadakar da mata hanyoyin da za su bi wajen gudanar da rayuwarsu kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya karantar, musamman dangane da zaman aure.
An kuma yi bayanin yadda iyaye mata za su tafiyar da tarbiyyar ’ya’yansu a matsayinsu na malaman farko da ke ba al’umma tarbiyya.
An gudanar da taron ne a Masallacin Cibiyar Kula da Addinin Musulunci da ke garin Damaturu a makon jiya.
Shugabar kungiyar reshen Jihar Yobe Hauwa Buba ta ce, neman ilmi wajibi ga dukkan al’umma musamman mata, wadanda tarbiyyar al’umma ke hannunsu.
Ta ce: “Idan ka karantar da mace daya tamkar ka karantar da rabin al’umma ne ko ma al’umma gaba daya.”
Ta ce kungiyarsu za ta yi fafutuka wajen ganin ta rika shirya  wa’azi ta hanyar gayyato malamai don fadakar da mata, kasancewar mace guda in ta lalace takan iya halaka mutane da yawa.
Ta bukaci magidanta su rika kokarin sauke nauyin da ke kansu na kula da matansu da kuma ’ya’yansu.
“Idan magidanta suka sauke nauyin da ke kansu, to kuwa mummunar dabi’ar nan da ta yi kaka-gida cikin al’umma na dora tallace-tallacen da ba su da dalili kan iya zama tarihi, kasancewar mafi yawa daga  tallace-tallacen da iyaye mata ke dora wa ’ya’yan kan taso ne a duk lokacin da aka yi rashin sa’a maigida ya gaza sauke nauyin da ke kansa na ciyarwa da tufatarwa da makamantan hakan.”
Ta ce mafi yawan lalacewar ’ya’ya mata da ake samu a arewa kan faru ne a sanadiyyar dora tallace-tallace, wadda a karshe in sun hadu da lalatattun maza sai su yaudare su har su rika yi musu fyade.
A karshe ta ce lokaci zuwa lokaci kungiyarsu ke rarraba kayayyakin abinci da sutura ga matan da suka rasa mazajen su da kuma yara marayu, domin su samu saukin gudanar da rayuwarsu.