✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An diba wa ’yan kwallon Tornadoes wa’adin wasa uku

A shekaranjiya Laraba ce mahukunta kulob din Neja Tornadoes de ke Minna suka diba wa daukacin ’yan kwallon kulob din da masu horar da su…

A shekaranjiya Laraba ce mahukunta kulob din Neja Tornadoes de ke Minna suka diba wa daukacin ’yan kwallon kulob din da masu horar da su wa’adin wasa uku su yi abin kirki ko a dauki mataki a kansu.

A wata takarda da Sakataren kulob din Malam Aliyu Mu’azu ya fitar aka raba wa manema labarai ta ce Shugaban kulob din Malam Abubakar Mustapha Gawu ne ya amince da daukar wannan mataki don ganin kulob din bai samu koma-baya a karshen kakar wasa ta  bana ba.

A gasar rukuni-rukuni ta bana, Neja Tornadoes na fuskantar matsala inda ake doke su gida da waje a wani lokaci kuma da kyar suke syin kunnen doki a wasansu na gida.

Shugaban kulob din Malam Abubakar ya ce ganin yadda kulob din ke tangal-tangal ya sa mahukunta kulob din suka dauki wannan mataki, kuma matakin zai fara ne a wasan da kulob din zai yi da Lobi Stars na Makurdi a wasa na 13.

Ya ce idan ’yan kwallon da jami’ansu ba su ci gaba da jajircewa da nuna kwazo ba, ko shakka babu za a dauki mataki a kansu.

Ya ce Neja Tornadoes ba karamin kulob ba ne da zai rika fuskantar irin wadannan matsaloli duk da zaratan ’yan wasan da yake takama da su.  “A gaskiya magoya bayanmu da mahukunta kulob din ba su ji dadin halin da kulob din yake ciki a yanzu ba, don haka muka yanke shawarar daukar wannan mataki,” inji shi.

Kawo yanzu Neja Tornadoes ke matsayi na karshe a teburin gasar rukunin mai kungiyoyi 12.

Alamu sun nuna kulob din zai iya samun koma-baya a karshen kakar wasa ta bana wanda hakan ne ya sa kulob din ya dauki wannan mataki.