Gwamnatin mulkin soji a Burkina Faso ta ce hukumomi leƙen asiri sun daƙile wani yunƙurin kifar da gwamnatin a cikin watan Afrilu.
Ta ce an aka kitsa juyin mulkin ne domin haifar da ruɗani a kasar ta yammacin Afirka.
Ministan tsaro, Mahamadou Sana ya ce wasu sojojin da ke cikin kaki yanzu da kuma waɗanda suka yi ritaya ne suka jagoranci yuƙurin juyin mulkin.
Gwamnatin ta ce an gano waɗanda suka shirya juyin mulkin daga makwabciyarta Ivory Coast.
Shugaban gwamnatin rikon kwarya Ibrahim Traore Kaptin ɗin soja wanda shi kansa ya hau shugabanci ne ta hanyar juyin mulki a 2022 ya sha zargin ƙasar Ivory Coast da bai wa masu adawa da shi mafaka.