✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dawo da ‘yan Najeriya 160 da suka makale a Libya

Ma’aikatar Harkokin Waje ta sanar da dawowar wasu ‘yan Najeriya 160 da suka makale a Tripoli, babban birnin Libya. Bolaji Akinremi, Daraktan ofishin jakadanci da…

Ma’aikatar Harkokin Waje ta sanar da dawowar wasu ‘yan Najeriya 160 da suka makale a Tripoli, babban birnin Libya.

Bolaji Akinremi, Daraktan ofishin jakadanci da sashen shari’a na ma’aikatar ne ya karbi wadanda suka dawo da safiar Laraba a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Mista Akinremi ya ce, “wadanda suka makale a kasar Libya sun hadar da manya 98 da kuma kananan yara 62.

“Jami’an Ma’aikatar Harkokin Waje, Hukumar Lura da ‘Yan Najeriya Mazauna Ketarer (NIDCOM), Hukumar Shige da Fice da kuma Hukumar Dakile Cututtuka Masu Taduwa NCDC sun karbe su lokacin da suka dawo, don tabbatar da sun bi matakan dakile yaduwar cutar COVID-19,” a cewar Akinremi.

Ya kara da cewa, dawo da ‘yan Najeriyar da suka makale ya tabbata ne a sakamakon wani aikin hadin gwiwa tsakanin Gwamnatin Najeriya da kuma Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM).

Aminiya ta samu cewa za a killace wadanda suka dawo Najeriya a sansanin Alhazai da ke Abuja, inda za su kwashe kwanaki 14 kamar yadda dokokin dakile yaduwar cutar COVID-19 suka tanada.

Shugabar Hukumar NIDCOM, Abike Dabiri-Erewa, ta yaba wa duk wanda suka ruwa da tsaki wajen dawo da su gida, sannan ta gargadi mutane da su guji yin tafiye-tafiye da suke cike da hadari.