Da misalin ƙarfe 11.30 kafin wayewar ranar Asabar din nan aka dawo da wutar lantarki a Jihar Kaduna.
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna (Kaduna Electric) ya dawo da wutar be bayan kwanaki babu ita.
An dauke wutar ne sakamakon yajin aiki da ma’aikatansa suka shiga tsawon kwana biyar.
Kaduna Electric ne ke ba da wutar lantarki a Jihar Kaduna, Sokoto, Zamfara da Kebbi.
Ma’aikaran sun janye yajin aikin ne bayan Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani ya shiga tsakaninsu da kamfanin.
Uba Sani ya bayyana wa masu yajin aikin irin mummunan halin da al’ummar suka shiga na rashin ruwan sha da durƙushewar harkokin rayuwa a sakamakon rashin wutar.