✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An dawo da littafin da aka sace a dakin karatu bayan shekara 50

An sace littafin ne a jihar Ohio ta Amurka

Mahukunta dakin karatu na garin Cincinati da ke Jihar Ohio a Amurka sun ce, an dawo da wani littafi da aka ara bayan shekara 50 wanda da farko suka dauka an sace shi.

Littafin mai suna ‘Tarzan and the Tarzan Twins’ wanda marubuci Edgar Rice Burroughs ya rubuta, an dawo da shi dakin karatun dauke da wata karamar takarda da ta yi bayanin yadda littafin ya yi batan dabo.

Takardar dauke da rubutu kamar haka: “Ga duk wanda ya samu wannan, na dawo da wannan littafi ne da na ara tun a 1972 ko 1973, lokacin ina matashi. Ina fatan za a same shi cikin yanayi mai kyau. Na dawo da shi saboda na kasa dawo da shi a tsawon wadannan shekaru,” kamar yadda aka rubuta a jikin takardar da ke kunshe a jikin littafin.

Wani ma’aikacin dakin karatun na Cincinati mai suna Brian Powers ya ce, sun yi farin cikin da aka dawo da littafin wanda ya shafe tsawon shekara 50 da bacewa.

“A jikin takardar ya bayyana shekarar da ya dauki littafin, amma bai bayyana dalilin da ya sa ya dawo da shi ba.

“Watakila ya ji ba dadi ne shi ya sa ya dawo da littafin ko kuma ya samu labarin ba ma karbar karin kudi idan mutum bai dawo da littafi a kan lokaci ba. Watakila shi ne dalilin da ya sa ya dawo da shi bayan shafe wadannan shekaru a tare da shi,” inji shi.

Powers ya ce, za a mayar da littafin cikin jerin littattafan dakin karatun don mutane su ci gaba da amfana da shi.

“Zan mayar da shi cikin littattafanmu, littafin ya fito a 1963 kuma ya shekara 50 a tare da mu, yanzu kuma zai koma gidansa kamar da, abin farin ciki ne an dawo da shi domin wani zai amfana da shi,” inji shi.

%d bloggers like this: