Gwamnatin Jihar Kaduna ta dage dokar katse hanyoyin sadarwar da ta yi tun a watan Oktoba saboda hare-haren da ’yan bindiga suke kai wa wasu sassan Jihar.
Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan a ranar Juma’a.
- Tinubu ya je Kano domin ta’aziyyar rasuwar kanin Dangote
- Buhari ya umarci a fatattaki ’yan bindiga daga hanyar Kaduna zuwa Abuja
A cewarsa, tuni Gwamnatin Jihar ta umarci kamfanonin sadarwa da su dawo da hanyoyin sadarwar da aka riga aka katse a baya.
A watan Oktoba ne dai gwamnatin ta dauki matakin katse layukan wayar a wasu sassan Jihar sakamakon yadda al’amarin rashin tsaro ya yi kamari a wasu yankunan Jihar.
Sai dai kuma duk da haka, matakin bai hana ’yan bindigar ci gaba da kai hare-hare ba, musamman a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Sai dai kuma Gwamnatin ta ce sauran matakan da ta dauka kamar na hana hawa babura da hana cin kasuwannin mako-mako da kuma sayar da man fetur cikin jarkoki har yanzu na nan daram.