Kotu ta yanke wa mutumin da ya kitsa garkuwa da kuma sayar da wasu kanaan yara a Jihar Kano hukuncin daurin shekara 104 a gidan yari.
Babbar Kotun Jihar Kano ta kama mutumin ne da laifin sacewa da kuma sayar da wasu kananan yara shida ’yan kasa da shekaru 10 a Jihar Kano tare da sayar da su a garin Onitsha, Jihar Anambra.
- An kama matashin da ya kashe karuwa yana ciniki da wata
- Najeriya ba ta san da sayen makaman $875 daga Amurka ba —Minista
Alkalin Kotun, Mai Shari’a Zuwaira Yusuf ta yanke hukuncin ne a ranar Juma’a bayan kama shi da laifuka 38 da gwamnatin jihar ta gurfanar da shi a kansu kamar yadda mai magana da yawun bangaren shari’a na Jihar Kano, Baba Jibo ya yi bayani.
Alkalin kotun ta raba hukuncin ne zuwa ga gida uku; a kashi na farko alkalin ta same da laifuka shida wanda a kan kowanne ta yanke masa hukuncin daurin shekara bakwai, daya-bayan daya — shekara 42 ke nan — da kuma karin tarar Naira 100,00 ba tare da zabi ba.
Rukuni na biyu kuma laifuka bakwai aka kama shi da aikatawa, kuma kowane laifi daurin shekara bakwai ba tare da zabi ba — Jumulla shekara 49 ke nan.
A rukuni na uku kuma kotun ta kama shi da laifuka biyu, kuma kowanne ta yanke masa hukuncin daurin shekara biyar — shekara 20 ke nan — ba tare da zabi ba.
Hukuncin da Kotun ta yanke ya ce mutumin zai yi shekara 104 ne daya-bayan daya.
Sauran mutum biyar da ake zargi tare da shi kuma sun ki amsa laifin, kuma nan gaba za a ci gaba da shari’arsu.
Alkalin ta ba da umarnin a tsare su a gidan yarin zuwa lokacin da za a ci gaba da shari’ar.