Tsoho dan shekara 70 zai kwashe shekaru 30 gidan kaso tare da aiki mai tsanani bisa hukuncin kotun ta yanke masa na fyade da ya yi wa yarinya ‘yar shekara tara a garin Minna na Jihar Neija.
Dan sanda mai gabatar da kara, ya gabatar da shaidu biyu a gaban kotu da suka hada da wadda aka yi wa fyade da kuma dan sandan da ya dauki jawabin tsohon na amincewa da yi wa yarinyar fyade.
Da take gabatar da shaida, yarinyar ta ce tsohon ya yi mata fyade sau biyu tare da tsoratar da ita cewa zai tura mata maciji a idan ta fada wa wani, sannan ya ba ta naira 50.
A tashi shaidar, an sanda da ya dauki jawabi a caji ofis ya tabbatar wa kotu cewar mai laifin amsa aikata fyaden.
“Mohammed Sani ya amsa aikata fyaden, kuma binciken asibiti ya nuna an keta wa yarinyar budurci” inji dan sandan.
Haka nan kuma wanda ake zargin, Sani, bai musanta duk abubuwan da aka zarge su da su ba.
Bayan ya amsa laifinsa, Mai Shari’a Safuratu Abdulkareem Mahmud ta yanke masa hukuncin daurin shekara 30 a gidan kaso ba tare da zabin tara ba.
Alkalin ta ce, hukuncin ya yi daidai ne da sashe na 18, sakin layi na 2 a dokar yancin yara kanana (2010) na Jihar Neja.
Daga jin hukumci da aka yanke, sai Sani ya yi wuf ya ce, “Ina son ta, kuma zan daukaka karar wannan hukunci da aka yanke”.
A kwanakin da suka wuce ne aka kama tsohon bayan da mahaifiyar yarinyar ta fahimci fitar tata na cikin damuwa.
Da ta tambayi yarinyar ne ta fada mata cewar mutumin ne ya yi mata fyade, Wanda hakan ya sa aka kama shi.