✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daure matasan da suka saci masara a injin nika

Hukumar Tsaro ta Sibil Difens ta gabatar da wadansu matasa uku a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da Tashar Babiye a cikin garin Bauchi bisa zarginsu…

Hukumar Tsaro ta Sibil Difens ta gabatar da wadansu matasa uku a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da Tashar Babiye a cikin garin Bauchi bisa zarginsu da sace masara mudu 40 a wani injin nika a Unguwar Bayan Gari da ke garin Bauchi.
Lauya mai gabatar da kara Barista B. Daikup ya bayyana wa kotun cewa wadanda ake zargin sun hada da Abdul’aziz Adamu da Shamsudden Musa da Abdulmumini Ibrahim kuma dukkansu suna da zaune ne a cikin garin Bauchi.
Sai dai kuma da kotu ta tambayi wadanda ake zargin ko sun aikata haka sun bayyana cewa tabbas sun saci masara mudu 40 a injin nika sakamakon yadda talauci da rashin aikin yi suka addabe su, amma suna rokon kotu ta yi musu sassauci.
daya daga cikin wadand ake zargin Abdul’aziz Adamu ya bayyana wa kotun cewa babu wanda yake da mace a cikinsu kuma rashin sana’a ce tasa suka saci masarar sun kuma sayar da ita ce a kan Naira 2,300.
Alkalin Kotun Mai shari’a Is’hak Magani ya yanke musu hukuncin biyan tarar Naira dubu biyar-biyar ko kuma su yi zaman gidan kurkuku na wata uku-uku.
Daga bisani sun gagara biyan kudin tarar inda nan take aka tura su gidan kurkuku da ke Bauchi bayan sun gama zaman za su biya mai masarar kudinsa