Kotun shari’ar Musulunci da ke unguwar Danbare a Kano ta daure wani Mai Unguwa bisa zargin sace janareta da kofofi a wani kango.
An daure shi ne bayan tuhumarsa da aikata laifukan shiga wuri ba da izini ba, da kuma sata.
- Ambaliya ta lalata gidaje kusan 150 a Jos
- An lakada wa Kwamishina duka a wajen rabon kayan tallafi a Ondo
Tun da fari dai dan sanda mai gabatar da kara Insfekta Bashir, ya shaida wa kotun cewa Rundunar ’Yan Sandan ta kamo mai unguwar ne bayan wani bakanike ya kai musu rahoton sace masa janareta da wasu kayyakin a kangon da yake gudanar da sana’arsa.
Daga nan ne kuma bincike ya kai su ga kamo mai unguwar suka kuma gurfanar da shi a gaban kotun. To sai dai mai unguwar ya musanta zargin.
Alkalin kotun, Munzali Idris Gwadabe ya ba da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan yari, sannan ya daga shari’ar zuwa ranar 18 ga watan Oktoba.