✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daure Fasto shekara daya saboda neman matar aure

Wata Kotun Majistare da ke garin Bwari, Abuja ta yanke hukuncin daurin shekara daya da rabi ga wani Fasto, bayan ta same shi da aikata…

Wata Kotun Majistare da ke garin Bwari, Abuja ta yanke hukuncin daurin shekara daya da rabi ga wani Fasto, bayan ta same shi da aikata laifin mu’amala da matar aure da kuma yin barazanar kisa ga mijinta saboda ya ja masa kunne.

Fasto Oladele Taiwo, wanda jagoran wata majami’a ce kuma mazaunin Unguwar Sabon-Gari a garin Bwari, kotun ta same shi ne da aikata laifuffuka uku da suka hada da shiga muhalli ba tare da izinin mai shi ba da yaudarar matar aure da kuma yin barazana ga mijinta, laifuffukan da suka saba dokoki na 342 da na 387 da kuma na 397 a tsarin dokoki na Final Kod.

Da yake zartar da hukuncin a ranar Litinin da ta gabata, Mai shari’a Abdullahi Ahmad Ilelah ya ce bayan shigar da karar a ranar 16 ga Junairun bara da mijin matar ya gabatar, kotun ta ba da umarnin gudanar da bincike a kan korafin wanda ’yan sandan shiyya da ke garin Kubwa suka gudanar.

Ya ce daga nan ne kuma sai kotun ta gayyaci shaidu don su ba da bahasinsu a kan lamarin kamar yadda shari’a ta bukata, inda a karshe kotun ta gamsu ba tare da wani kokwanto ba cewa wanda aka yanke wa hukuncin ya aikata laifuffukan da aka zarge shi a kai. Alkalin ya ce a dalilin haka kotun ta yanke hukuncin daurin wata uku tare da zabin biyan tara a kan laifi na farko, sannan kuma ta yanke hukuncin daurin kwana 490 a kan laifuffuka na 2 da na 3 ba tare da zabin biyan tara ba.

Kafin zartar da hukuncin, kotun ta nemi jin ta bakin lauyansa a kan laifuffukan da aka same shi da aikatawa, inda lauyan mai suna Musima J. Belle ta roki kotun ta nuna jinkai ga mutumin ta hanyar sassauta masa hukunci, bukatar da lauyan mai shigar da kara mai suna Diana Mba ba ta yi jayayya a kai ba.

Da yake tsokaci a kan lamarin kafin wucewa da shi zuwa kurkukun garin Suleja, Faston ya bayyana mamaki a kan shari’ar. Ya ce Ubangiji da kanSa zai daukaka hukuncin da kotun ta zartar.