Kotu ta yanke wa wani fasto hukuncin daurin rai-da-rai kan laifin yi wa ’ya’yan abokinsa tagwaye masu shekara 12 fyade.
Kotun hukunta laifuka cin zarafi ta yanke wa Fasto Michael Oliseh mai shekara 54 hukuncin ne bayan ta gano yadda ya rika yi wa tagwayen fyade a lokuta daban-daban.
- ‘Cin zarafin mata na karuwa a kafofin sadarwa na zamani a Najeriya’
- Sojoji sun tsere bayan harin ISWAP a Chibok
Alkalin kotun, Mai Shari’a Abiola Soladoye ta ce, “Shaidun da aka gabatar sun tabbatar da yadda wanda ake zargin ya kasance yana yawan yi musu fyade a lokuta daban-daban.
“Amma wannan akwai faston banza maciyin amana, babu kunya ya rika yi wa ’ya’yan abokinsa da ya ba shi amanar su fyade. Ba a san fasto da irin haka ba.”
Gabanin haka, mai gabatar da kara, Misis Olufunke Adegoke, ta shaida wa kotun cewa Oliseh ya lalata tagwayen ne bayan mahaifinsu ya bar mishi su ya yi tafiya zuwa kauye domin halartar jana’iza a watan Nuwamban 2017.
Ta kara da cewa bayan Oliseh ya lalata yaran, ya yi musu barazana cewa idan suka kuskura wani ya san abin da ya yi musu, to mahaifinsu zai rasa aikinsa.
Ta bayyana wa kotun cewa dubuna ta cika ne baya ya bi daya daga cikin yaran gidan makwabta ya cakumo ta dan kamfenta.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Abiola Soladoye ta bayyana cewa masu shigar da kara su gabatar da gamsassun hujjoji da ke tabbatar da yadda faston ya rika yi wa kananan yaran fyade.
Ta kuma ba da umarnin sanya sunan Fasto Micheal, wanda shi ne na’ibin faston cocin Anointed Chosen Vessel Ministry, da ke Okota a Jihar Legas, a rajistar mutanen da aka kama da lafin fyade na Jihar Legas.
Duk da haka ta kuma caccakin iyayen yaran da sakaci wajen bayar da amanar ’ya’yansu ga mutum mara kamun kai.
Ta bayyana cewa bai kamata a rika ba da amanar yara ga manya marasa kamun kai ba, “A rika bayar da kula da su ga mutanen da amana suka kuma damu da damuwarsu.”