✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An daure dillalan tabar wiwi a Kano

Kotun Majistare ta 32 da ke Gyadi-Gyadi a birnin Kano ta daure wadansu matasa biyu bisa samunsu da laifin sayar da tabar wiwi. dan sanda…

Kotun Majistare ta 32 da ke Gyadi-Gyadi a birnin Kano ta daure wadansu matasa biyu bisa samunsu da laifin sayar da tabar wiwi.

dan sanda mai gabatar da kara ASP Sani Musa ya shaida wa kotun cewa ’yan sandan da ke gudanar da aiki Tarauni a karkshin jagorancin Sufeto Ado Kabiru Kabara ne suka kama matasan da suka hada da Ibrahim Umar wanda aka fi sani da Boss da Mansur Musa, dukkansu mazauna Unguwar ’Yansana da ke karamar Hukumar Kunbotso, a inda suke sayar da tabar wiwi.

Mai gabatar da karar ya ci gaba da cewa, “An kama matasan da kullin tabar wiwi 172 da kuma wata wiwin a kulle a leda, kuma wadanda ake zargin sun amsa laifinsu na mallakar tabar wiwi; laifin da ya saba da sashe na 401  na Kundin Shari’ar Final Kod.

Mai shari’a Rahama Mu’azu ta yanke musu daurin shekara daya a gidan maza ba tare da zabin biyan tara ba.

A wani labarin kuma, kotun ta yanke wa wata mace mai suna Amina Haruna daurin wata biyu a kurkuku bisa zarginta da bayar da cin hanci ga ma’aikata.

Mai gabatar da kara ASP Sani Musa ya shaida wa kotun cewa wadda ake zargin, da ke zaune a Unguwar Na’ibawa, ta dauki Naira dubu 20 ta kai wa wani dan sanda mai suna Saje Madaki Muhammad, da ke aiki a ofishin ’yan sanda na Tarauni don a saki wani saurayinta mai suna Ibrahim Umar da aka kama da laifin sayar da tabar wiwi.