Wata kotu da ke zamanta a yankin Kasuwan Nama da ke garin Jos, a jihar Filato ta yanke wa wani dalibi hukuncin daurin wata shida a gidan yari saboda satar karnuka biyu.
Bayan amsa laifin da matashin ya yi, kwamitin alkalan da suka jagoranci shari’ar sun yanke masa hukuncin durain wata uku ko biyan tarar N20,000.
- Kwankwasiyya ta soki Ganduje kan yunkurin rushe gadar sama
- Zaman dar-dar: Dattawan Arewa za su gana da gwamnoni
- Satar doya ta jawo masa hukuncin bulala 12 a kotu
- An kama kani a cikin masu garkuwa da matar wansa a Zariya
Alkalan sun kuma bukaci ya biya diyyar N50,000 saboda satar karnukan, ko kuma ya sake shafe wasu watanni uku a daure.
Sun ce hukuncin da aka yanke wa dalibin mai shekara 15, zai zama izina ga masu yunkurin aikata irin laifi.
Tun da farko, lauyan da ya shigar da kara, Ibrahim Gokwat ya ce an kai kara ofishin ’yan sanda na Angwan Rogo a ranar 21 ga Janairu.
A cewar lauyan, darajar karnukan da dalibin ya sata ya kai N50,000 kuma hakan laifi a karkashin Sashe na 272 na Kundin Manyan Laifuka na Jihar Filato.