Sakamakon katsewar wutar lantarki a Pakistan, asibitoci da kamfanoni da sauran al’ummar kasar musamman na yankin Kudancin kasar na cikin mawuyacin hali.
A tattaunawarsa da gidan talabijin na Aljazeera, wani mai suna Muhammad Pervez ya ce mahaifinsa da ke fama da rashin lafiya ya kawo asibiti, sai dai ba abin da likitocin suka iya yi masa, saboda na’urorin sai da lantarki suke aiki.
- An guntule kan Shugaban Karamar Hukuma a Imo bayan karbar diyyar N6m
- Ganduje ya kaddamar da sabon ‘taken’ Jihar Kano
“Wasu manyan asibitocin na da injinan da ke bayar da wutar lantarki, amma na talakawa irin wannan ko ganin likitan ma aiki ne saboda duhu, tunda ko na’urorin aikin ma ba duka suke da su ba.”
Shi ma wani Manajan Daraktan wani kamfani mai suna Kamran Arshad, ya ce sai rufe kamfaninsa ya yi ranar Litinin saboda lalacewar wutar.
“Kaso 60 na ayyukanmu da wutar lantarki muke yi, kaso 40 ne kadai muke iya yi da janareta. To shi ma man janaretan ya yi tsada, don haka rashin wutar ya sa sai rufewa muka yi.”
Arshad ya ce asarar da suka tafka sakamkaon hakan ta haura ta biliyoyi.
“Asarar da muka yi a rana daya kacal ya kai na Dala 87. Kuma idan aka hada duka rassan kamfanoninmu dake kasar mun yi asarar biliyoyin Rupee.
Su ma dai jami’an asibitin Karachi Jinnah (JPMC) daya daga cikin asibitocin da suka fi kowanne girma a Pakistan, ya ce suna da hanyoyin aiki zuwa wani lokaci ko ba wutar lantarkin.
Wannan dai shi ne karo na biyu a watanni hudu da kasar ta samu irin wannan matsalar har ta tsawon fiye da sa’o’i 12 a yankin Kudancin kasar.
Sai dai ma’aikatar makamashi ta kasar ta fitar da wata sanarwa ta shafinta na Twitter, inda ta ce wutar kasar ta lalace ne da karfe 7:34 na safiya ranar Litinin, kuma za ta kwashi sa’o’i 12 kafin ta dawo aiki.