Hankalin masu motoci a Faransa ya kara tashi sakamakon cunkoson ababen hawa a gidajen man kasar saboda karancin man fetur da yajin aikin da ma’aikatan kamfanin mai na kasar ke yi.
Yajin da ma’aikatan kamfanin man fetur na Total Energies ke yi, a ranar Juma’a ya shiga rana ta 12, wanda tsawon hakan ya sa abin da gidanjen man kamfanin 3,500 ya dauko karewa, yanayin da ya tayar wa da ’yan kasar hankali.
- Ana sace gangar danyen mai 900,000 kullum a Najeriya —Lawan
- Tarayyar Afirka ta taya Macron murnar sake lashe zaben Faransa
- Za a rufe shafukan batsa a Faransa
A wani sako da wani dan Faransa ya sanya dandalin sada zumunta na Facebook, ya ce, “Shin akwai wanda ya san wani gidan mai da ke bayar da mai, ko kuma ya ga ana sauke masa mai?”
“Don Allah a ina zan samu mai?” A cewar wani sakon daban, wanda ke nuna halin ni-’yasun da mutanen kasar ke ciki na rashin mai, da fatan samun inda za a cika tanki saboda hutun karshen mako.
Ma’aikatan Totalenergies na yajin aikin ne domin su matsa wa kamfanin biya musu bukatarsu ta matsalar albashi.
Gwamnati ta sa a fitar da man fetur daga rumbun ajiyar manta don cike gibin, a cewar Ministar Makamashi ta Faransa, Agnes Pannier-Runcher a hirarta da gidan talbijin na FMTV a ranar Alhamis.