✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An datse kan wani dan acaba a Kurosriba

Fadan kabilanci tsakanin kabilun Ediba da na Usumotong da ke kananan hukumomin Abi da Yakurr a Jihar Kurosriba ya yi sanadin da wasu ’yan ta’adda…

Fadan kabilanci tsakanin kabilun Ediba da na Usumotong da ke kananan hukumomin Abi da Yakurr a Jihar Kurosriba ya yi sanadin da wasu ’yan ta’adda da ba a shaida ba suka dauki fansa, suka yi wa wani dan acaba mai suna Eric Omori Ewa, dan shekara 32 da haihuwa yankan rago, inda suka datse masa kai suka tafi da shi.

Lamarin ya faru ne bayan da makisan suka yi masa   kwanton bauna lokacin da ya dauko wasu mata uku a kan babur, zai kai su kasuwar Ugep da ke karamar Hukumar Yakurr. Makisan, kamar yadda wata majiya ta shaida mana, ana zargin daga kauyen Ediba suke, suka tare hanyar da dan acabar ya taho, wadda babu wata hanya da ake bi, musamman ga mutanen kauyen Usumutong, idan za su cin kasuwar Ugep.

Joseph Omini Ogburuwa, makwabcin wanda aka kashe, ya shaida wa Aminiya a Kalaba cewa: “Al’ummar kauyen Ebom da na Ediba ne suka tare hanya dauke da muggan makamai, mamacin yana zuwa daidai inda suke, suka buge shi ya fado daga kan babur din, suka kashe shi suka cire masa kai suka tafi da shi, suka bar gangar jikin. Matan da yake dauke da su kuma suka gudu saboda tsoron abin da ya faru.”

daya daga cikin matan da aka harba a kafa, Peace Enyieko, ta sanar wa wakilinmu cewa, ita da ’yar uwarta mai suna Juliet Dabid Osim da Ruth Osim Tom da dan acaban ya dauko duk da sun gudu domin su tsira da rayuwarsu. Maharani sun bi su suka harbe su, wata a kafada, wata a baya. Sauran mutane da suka biyo hanya suka tsinakyi abin da ke gudana, suka yanki daji suna gudu domin su tsira da rayukansu.

Wani mazaunin kauyen Ebom mai suna Kwamared Ogburuwa ya ce DPO maai kula da ofishin ’yan sanda na Ugep da abokin aikinsa DPO mai kula da ofishin   Itigidi, karamar Hukumar Abi sun je kauyen Usumutong, domin gane wa idonsu barnar da aka yi. Sun kuma ga gawar wanda aka datse wa kai, sun tabbatar wa a’lummar Usumutong cewa ’yan sanda na bin kadin lamarin kisan da kuma matan uku da aka sara. Ya ci gaba da cewa, duk da kasancewa ’yan sanda sun gayyaci sarakuna da shugaban matasa na Ediba su zo su yi mata bayani domin a zakulo makasan Ewa, lauyan al’ummar, Barista Essien Andrew ya shiga cikin maganar. Ya nemi ’yan sanda su yi wa mutanen Ediba hanzarin ba su lokaci su shirya zuwa gaban ’yan sandan domin su yi musu bayanin da suke nema.