✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dakile yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo

An tsare wanda ake zargin da kitsa juyin mulkin.

Gwamnatin Jamhuriyar Dimokuradiyar Kongo ta cafke mai ba wa shugaban kasar shawara kan harkokin tsaro bisa zargin yunkurin juyin mulki.

Gwamnatin ta bankado yunkurin kifar da ita da Francois Beya, ya yi tare da hadin gwiwar wasu jami’an gwamnatin kasar.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Felix Tshisekedi ne, ya bayyana wa manema labarai cewar ana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin a matakai daban-daban.

A ranar Asabar da ta gabata ne aka kama Francois Beya, mashawarcin Shugaba Tshisekedi kan harkokin tsaro saboda yunkurin kawar da shugaban wanda ya halarci taron shugabannin kasashen Afirka a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

Tshisekedi ya katse halartar taron inda ya koma gida a daren Asabar tare da tawagarsa.

Shugaban lauyoyin Kongo, Georges Kaplamba, ya ce ya ziyarci Beya a inda ake tsare da shi, kuma ana ci gaba da yi masa tambayoyi ba tare da tauye masa hakkokinsa ba.

Sai dai ya zuwa yanzu gwamnatin kasar ba ta fitar da sanarwa game da abin da bincikenta ya gano mata ba.

Amma jama’ar kasar na ci gaba da tsimayen sakamakon binciken da ake gudanarwa kan mai ba wa shugaban kasar shawara.