Rundunar tsaro ta ‘Operation Safe Haven’ (OPSH) ta dakile yunkurin yin garkuwa da fasinjojin wata mota a kan hanyar Barde zuwa Unguwan Ayaba da ke Karamar Hukumar Jama’a ta Jihar Kaduna.
Sojojin sun kuma sami nasarar kubutar da mutum shida daga hannun ’yan bindigar.
- Mahara sun kashe mutum daya, sun kona gidaje da motoci a Zangon Kataf
- Kishi ya sa wata mata cinna wa kanta wuta a Jigawa
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ya raba wa manema labarai ranar Asabar a Kaduna.
A cewar sanarwar, motar, wacce ta fasinjoji ce ta fito ne daga Abuja, inda bayan sanar da jami’an tsaro, sojoji suka yi nasarar kwato wasu mutane biyar daga hannun masu garkuwar.
Wadanda aka kubutar din sun hada da Bilkisu Umar da Maryam Usman da Abdulsalam Mohammad da Adamu Abdullahi da kuma Nafisa Abdulmumini wacce take tare da karamin yaro.
Kazalika, rundunar ta kuma yi nasarar kubutar da wani mai suna David Danladi daga hannun masu garkuwa a kan hangar Fanock zuwa Kyayya, shi ma a Karamar Hukumar ta Jama’a, a kan hanyarsu ta zuwa Keffi a Jihar Nasarawa.
Sojojin, sun kubutar da David ne daga motar masu garkuwar bayan ya samu rauni a kafarsa, inda tuni suka wuce da shi zuwa asibiti don yi masa magani.
A karshen sanarwar, gwamnatin Jihar Kaduna ta jinjina wa rundunar bisa namijin kokarin da tayi na dakile garkuwar da kuma na kubutar da mutanen da ta yi.