Hukumomin kasar Saudiyya sun dakatar da yin sallah a dukkan masallatan kasar, sai dai masallacin Ka’abah da kuma na Madina, kamar yadda kamfanin dillacin labaran kasar ya sanar.
A baya dai mahukuntan Saudiyya sun hana masu zuwa aikin Umrah da na Hajji shiga kasar saboda yaduwar cutar kurona.
Mutum 133 aka tabbatar sun kamu da cutar kurona a Saudiyya.
Rahoton BBC