Hukumar kula da ’yan wasan tsalle-tsalle ta sanar da dakatar da ’yar wasan tseren, Nzubechi Grace Nwokocha, saboda zargin amfani da haramtattun kwayoyi.
Cikin sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, Athletics Integrity Unit (AIU) ta ce dakatar da ’yar wasan mai shekara 21 bayan samun burbushin kwayoyin Ostarine da Ligandrol a cikin jinin Nwokocha bayan gwajin da aka yi mata.
- Matashi ya nutse a ruwa yayin ceto saniya a Jigawa
- Sanata Lawal da Gwamna Buni sun bude sabuwar Kasuwar Gashua
“AIU ta dakatar da ’yar tseren Najeriya Nzubechi Grace Nwokocha saboda amfani ko kuma samun kwayoyin da aka hana amfani da su a jikinta (Ostarine da Ligandrol),” a cewar AIU.
Hakan na nufin ba za ta sake shiga wasanni ba har sai an yanke hukuncin karshe yayin zaman da za a yi karkashin jagoranci da dokokin Hukumar Hana Zamba a wasanni ta WADA.
Ana fargabar akwai yiwuwar a kwace kyautar zinariyar da Najeriya ta samu a tseren.
Nwokocha tana cikin tawagar ’yan mata hudu – Tobi Amusan da Favour Ofili da Rose Chukwuma – wadanda suka lashe lambar zinare a gasar kasashen rainon Ingila ta 2022 a wasan tsere na tsallake shinge.
A watan da ya gabata ne Nwokocha ta lashe lambar zinare a tseren da ta doke abokan karawarta na Ingila da Jamaica.