✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2024 Olympic: ’Yar tseren Najeriya ta doke Amurka da Jamaica

Amusan ta doke Amura da Jamaica a kwata-final na gasar tasren mata ta mita 100 a wasannin Olmpic 2024 a kasar Farasa

Gwarzuwar ’yar Najeriya, Oluwatobiloba Amusan, ta lashe zagayen kwata-fainal a tasren mata na mita 100 a wasannin 2024 Olympic da ke gudana a kasar Farasa.

Amusan ta tsallaka zuwa zagayen semi-fainal a fafatawar ne baya ta kammala tseren Kwata-Fainal a cikin mintoci 12.49 inda ta doke Alaysha Johnson ta kasar Amurka da tazarar dakikoki 12.

Alaysha Johnson ce ta biyu, inda kammala tsaren cikin mintoci 12.61, sai Janeek Brown daga kasar Jamaica ce ta zo ta biyo baya da mintoci 12.84.

Amusan da su ukun da sauran wasu 12, ciki har da gwarzuwar Olympic, Jasmine Camacho-Quinn daga kasar Puerto Rico, ne za su fafata ranar Juma’a a zagayen kusa da na karshe.

Sauran wadanda za a fafata da su su ne gwaraza uku da za a samu har zuwa ranar Alhamis.

Za a yi tseren zagaye na garshe a gasar ne a ranar Asabar inda za a samu gwaruwar wannan shekara.