Kungiyar magoya bayan Nasarawa United a Jihar Nasarawa ta dakatar da shugabanta Salisu Galadima da aka fi sani da Atakinbasira da kuma Sakatarensa Abdulsalami Abubakar saboda zargin da ake musu na yin wadaka da kudin kungiyar.
A wata sanarwa da ta samu amincewar bakwai daga cikin wakilai 10 na kungiyar, an zargi shugaban ne watau Salisu Galadima da yin wadaka da kudin kungiyar kuma ana zarginsa da laifin karbar kudi daga hannun ‘yan wasa a lokacin shirin tantace su.
Sanarwar ta ce wannan dalilai ne suka sa mambobin kungiyar suka dauki matakin dakatar da shi tare da sakatarensa.
Sanarwar ta ce tuni aka nada Jamilu Yakubu a matsayin shugaban riko na kungiyar da Usman Aliyu Muhammed a matsayin sakatare kafin a kammala binciken da ake musu.
Ahalin da ake ciki hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa na Nasarawa United ta dauki matakin warware matsalar don tuni ta kafa kwamitin da ke kunshe da mutum uku don gudanar da bincike akan zargin da ake wa shugabannin kungiyar. Muhammad Alkali ne shugaban kwamitin binciken sai Hamza Ilayo a matsayin mamba yayin da Lauren Shemaa yake a matsayin sakatare.
A wani labarin kungiyar kwallon kafa ta mata a Jihar Nasarawa da aka fi sani da Nasarawa Amazons ta yi nasarar zama zakara a gasar Premier na kasa bangaren mata na shekarar 2013.
kungiyar ta samu nasarar ce a karshen mako da ya gabata a filin wasa na Lokaja Jihar Kogi inda ta doke ‘yan wasan Ribers Angels na Fatakwal da ci 4 da 2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
An dakatar da shugaban kungiyar magoya bayan Nasarawa United …Yayin da Nasarawa Amazons ta lashe gasar Premier
Kungiyar magoya bayan Nasarawa United a Jihar Nasarawa ta dakatar da shugabanta Salisu Galadima da aka fi sani da Atakinbasira da kuma Sakatarensa Abdulsalami Abubakar…
