✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dakatar da Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa na Kano, Muhuyi Rimin-Gado

An dakatar da Muhuyi ne kan tuhume-tuhume 10 da ke da alaƙa da cin hanci da rashawa.

Kotun Ɗa’ar Ma’aikata ta dakatar da Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar yada labaran kotun, Misis Veronica Kato ta fitar a ranar Alhamis a Abuja.

Ta ce an dakatar da Muhuyi ne kan tuhume-tuhume 10 da ke da alaƙa da cin hanci da rashawa da aka shigar a kansa a ranar 16 ga watan Nuwamban 2023.

“Da yake yanke hukuncin, alƙalin kotun, mai shari’a Danladi Umar, ya tabbatar da cewa kotun tana da hurumin sauraron karar da ake yi wa Muhuyi.

“Ya bayyana cewa doka ba ta bai wa Muhuyi Magaji damar ci gaba da tafiyar da al’amuran hukumar ba, yayin da yake fuskantar shari’a.

“Don haka an dakatar da shi har zuwa lokacin da za a kammala shari’a,” in ji Kato.

An dage sauraron karar zuwa ranakun 7 da 8 ga watan Mayu, 2024.