Gwamnatin Najeriya ta dakatar da ci gaba da allurar rigakafin Coronavirus kashi na biyu sakamakon wasu ayoyin tambaya da rashin tabbas da ke tattare da rigakafin.
Shugaban yada labarai a Ofishin Sakataren Gwamnati, Willie Bassey, ya shaida cewa matakin zai soma aike ne daga ranar Talata.
- Gwamnonin PDP za su yi taro kan makomar Shugaban Jam’iyyar
- Yajin Aiki: Gwamnati ta sa wa likitoci dokar ‘ba-aiki ba-albashi’
Sai dai sanarwa ta sa ba ta ba da cikakkun bayanai kan dalilan dage ci gaba da bayar da rigakafin ba.
Amma a cewarsa nan ba da jimawa ba za su sanar da ranar ci gaba da karbar allurar.
Aminiya ta ruwaito cewa, Gwamnatin Amurka ce ta ba da tallafin allurar rigakafin ga Najeriya kuma an kawo su ta hanyar COVAX a ranar 2 ga Agusta, 2021.
COVAX wani yunkuri ne na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya yi alkawarin samar da alluran rigakafin zuwa kashi 20 ga kasashen duniya.
Tun a watan Mayu Shugaban Amurka, Joe Biden ya yi alkawarin raba alluran rigakafin miliyan 80 ga kasashen duniya don kare marasa galihu, wadda ake sa ran Afirka za ta samu miliyan 25 daga cikin miliyan 80 da za a raba.
Sai dai binciken da Aminiya ta gudanar ta gano cewa, alluran rigakafin da aka kawo ba sa tare da shaidar tabbatar da an gudanar da cikakken bincike a kansu.
Haka kuma, kamfanin da ya hada rigakafin bai samu lasisi ba daga Hukumar Lafiya ta Duniya na tabbatar da ingancin hada magunguna.
Wadannan ayoyin tambaya da masana lamarin suka gano sun bayyana damuwa da kuma shakku a kan amincin rigakafin, musamman yadda aka nemi gwamnatin Najeriya ta sanya hannu kan wasu takardu na daukar alhakin duk wani abu da zai biyo baya.
Alkaluman Hukumar Dakile Cututtuka a Najeriya NCDC sun nun cewa, akalla mutum 53 cutar Coronavirus ta kashe cikin mako biyu a kasar.