Ma’aikatar Ilimi ta kasar Zimbabwe ta dakatar ta malaman makarantun da suka yi yajin aiki a ranar da dalibai suka koma makarantu.
Malamai da yawa a makarantun gwamnati a kasar sun yi yajin aiki ranar Litinin saboda karancin albashi.
- An kashe ’yan sanda 3 suna tsaka da binciken ababen hawa
- NAJERIYA A YAU: Tasirin Harshen Koyarwa Kan Neman Ilimi
An dakatar da malaman ne bayan sun shafe wata uku ba tare da an biya su albashi ba.
Gwamnatin Zimbabwe ta ce za a ci gaba da gudanar da bincike kan zargin rashin da’a da malaman da aka dakatar suka nuna.
Sai dai dakatar malaman bai yi mutane da dama dadi ba, inda wasu ke ganin hukuncin a matsayin rashin adalci.
Kungiyar malaman ta shiga yajin aikin ne tana neman a rika biyan su mafi karancin albashi na Dala 540.
Yawancin malaman makaranta a kasan ana biyan su kasa da Dala 200 a farashin gwamnati, wanda bai kai Dala 100 a kasuwar bayan-fage be, wadda yawanci da farashinta ake sayar da kaya da biyan ayyuka a kasar.
A ranar Talata gwamnati ta sanar da karin albashin ma’aikatanta da kashi 20 cikin 100, wanda ya hada da biyan su Dala 100 a wata.
An koma makarantu a kasar Zimbabwe ne a ranar Litinin bayan hutun wata daya a sakamakon cutar COVID-19.