✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dakatar da kwamishina kan abincin buɗa baki a Jigawa

An dakatar da kwamishinan har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zargin sama da faɗi da kuɗin abincin buɗa baki.

Gwamna Malam Umar A Namadi ya dakatar da Kwamishina a Ma’aikatar Kasuwanci ta Jigawa, Alhaji Aminu Kanta kan rabon abincin buɗa baki.

Aminiya ta ruwaito cewa, an dakatar da kwamishinan ne har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan rabon abincin buɗa baki a Karamar Hukumar Babura ta jihar.

Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jigawa, Malam Bala Ibrahim ya fitar a Yammacin wannan Juma’ar.

Sanarwar ta ce an ɗauki wannan mataki a ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke na tabbatar da gaskiya ta ƙeƙe da ƙeƙe a fannin gudanar da harkokin kuɗi

Tuni dai Gwamna Namadi ya ba da umarnin aike wa kwamishinan wasiƙar dakatarwar nan take.

Bayanai sun ce ana zargin kwamshinan da yin ruf da ciki kan wasu kuɗaɗe da aka ware domin gudanar da aikin ciyarwar buɗa baki a Karamar Hukumar Babura ta jihar.