Gwamnan Jihar Jigawa ya dakatar da Kwamishinansa da Hisbah ta kama bisa zargin kwartanci a Jihar Kano.
Kwamishinan Ayyuka na Jihar Jigawa, ya faɗa a hannun Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ne, bayan jami’anta sun kama shi da wata matar aure da ake zargin yana lalata da ita.
Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, ya amince da dakatar da kwamishinan nan take, har an kammala bincike ke zargin kwartanci da Hisbah take masa.
Sanarwar dakatarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya sanya wa hannu ta ce an dakatar da Kwamishinan ne domin kare martabar jihar da kuma tabbatar da adalci a kan lamarin.
- Sai dai APC ta kore ni, amma ba zan daina tsage gaskiya ba —Ndume
- Babban layin lantarki ya ɗauke karo na 4 cikin mako guda
“Dakatarwar tana daga cikin matakan da aka ɗauka domin tabbatar da adalci wajen bincike.
“Kowannenmu ya san girman irin wannan mummunan zargi, kuma a shirya muke cikin hattara domin tabbatar da sauke amanar da al’ummar Jihar Jigawa suka ɗora mana,” in ji sanarwar.
Aminiya ta ruwaito a cewa ’yan Hisbah sun kama kwamishinan da mota a wani kangon gini.
Dubunsa da matar auren ta cika ne bayan mijinta ya kai musu ƙorafi cewa yana zargin matar da cin amanar aure da kwamishinan.
Wani jami’in hukumar da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana wa Aminiya cewa sun kama kwamishinan da matar ne bayan jami’an Hisbar da mijin matar sun rutsa su a wani kango mallakin kwamishinan a cikin mota.
Ya ce, ganin su ke da wuya, sai matar mai ’ya’ya biyu ta yi yunƙurin tserewa a motar, inda ta buge mai gadin.
Amma ya bayyana cewa daga bisani rundunar ta samu nasarar tsayar da ita da nasu motocin.