Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da dakatar da Kwamandan Hisbah na Karamar Hukumar Dala, Malam Suyudi Hassan Muhammad bisa zargin sa da karkatar da kayan tallafin COVID-19.
Tun da farko dai an zargi kwamandan ne da karkatar da kayan tallafin wanda Karamar Hukumar ce ta bayar domin a rabawa jami’an hukumar don rage radadin annobar ta Corona.
- An dakatar da Kwamandan Hisbah kan karkatar da kayan tallafi
- Hisbah ta lalata kwalaben giya miliyan biyu a Kano
Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Malam Lawal Fagge shi ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya ranar Litinin.
Idan za a iya tunawa jami’an Hisba da ke aiki a ofishin hukumar a Karamar Hukumar Dala da yawansu ya kai 73 suka mika takardar korafi ga Hedikwatar Hukumar game da zargin da suke yi wa shugaban nasu na karkatar da kayan tallafin.
Malam Lawal ya kara da cewa Hukumar ta dauki wannan mataki ne biyo bayan shawarar da kwamitin da ta kafa don bincikar lamarin ya ba ta.
Har ila yau, kakakin ya kuma bayyana cewa dakatarwar da aka yi wa kwamandan za ta dauki tsawon wata guda.
“Bayan da suka kawo korafin Hukumar Hisba ta kafa karamin kwamiti da zai fara bincikar lamarin a mataki na farko, don haka wannan kwamitin ya bayar da shawarar dakatar da Kwamandan domin su samu damar zurfafa bincike a kansa,” inji shi.